
Shugaban Kasa, Bola Tinubu, ya umarci Rundunar Sojoji, Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da hukumomin leken asiri da su gaggauta fara wani samame na hadin gwiwa domin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a sabon harin satar jama’a a Jihar Niger, inda ya umarci shugabannin hukumomin tsaro su rika ba shi rahoton halin da ake ciki har sai an gano duk wadanda aka sace.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata a Abuja.
Tinubu ya nuna matukar bacin ransa kan sacewa da kashe fararen hula da miyagun laifuka suka yi a jihar, yana mai bayyana harin a matsayin abin takaici, dabbanci da kuma wanda ba za a amince da shi ba.
Ya ce, “Wadanda suka kai wannan mummunan hari kan ’yan Najeriya marasa makami, makiyan zaman lafiya ne da makiyan bil’adama, kuma ba za su tsira daga hukunci ba.”
Shugaban kasar ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda aka kashe a harin, tare da yin addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya ba mamatan hutu na har abada, Ya kuma ba iyalansu hakurin jure wannan babban rashi.
Ya tabbatar wa iyalan wadanda abin ya shafa cewa gwamnatin tarayya na nan kan bakarta wajen tabbatar da dawo da ’yan uwansu cikin aminci.
Tinubu ya ce, “Ba ku kadai ba ne. Dukkan kasa na tare da ku cikin wannan radadi. Ba za mu huta ba har sai an dawo muku da ’ya’yanku maza da mata, iyayenku mata da maza cikin aminci.”
Ya umarci Rundunar Sojoji, Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, Hukumar Tsaro ta DSS da sauran hukumomin tsaro da leken asiri da abin ya shafa su hada kai domin tabbatar da sakin wadanda aka sace.
Tinubu ya kuma umarci shugabannin hukumomin tsaro su rika sanar da shi duk wani sabon ci gaba har sai an tabbatar da makomar kowane mutum da aka yi garkuwa da shi.
Ya ce, “Ta’addanci ba zai tsoratar da Najeriya ba. Za mu kare al’ummarmu, mu kare garuruwanmu, tare da tabbatar da mutuncin rayuwar dan Adam.”
Shugaban kasar ya ce addu’arsa na tare da al’ummar Jihar Niger a wannan mawuyacin lokaci, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin tarayya na tare da gwamnatin jihar, kuma za ta bayar da dukkan tallafin da ya dace domin taimakawa wajen farfadowa, agaji da karfafa tsaro.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa a ranar Juma’a ne ’yan ta’adda suka mamaye wani masallaci da ke Gidan-Zana, kauyen Kpenya, gundumar Dekara, karamar hukumar Borgu ta Jihar Niger, inda suka yi awon gaba da dimbin masu ibada yayin sallar Juma’a.
NAN